Tattaunawa-logo

Tattaunawa

RFI France

More Information

Location:

United States

Genres:

Podcasts

Networks:

RFI France

Language:

English


Episodes

Ra'ayoyin Masu sauraro kan zanga zangar kin jinin China a kasar Zambiya - 25/09/2018

9/24/2018
More
Ra'ayoyin masu saurare, kan sanin ko kasancewar kasar china a kasuwanin nahiyar Afrika wani sabon salon mulkin mallaka ne, ta hanyar damfarawa kasashen nahiyar bashi kamar yadda kasashen yammaci ...

Duration:00:15:22

Majalisar dinkin duniya tace galibin makarantu a duniya basu da ruwan sha mai tsafta - 28/08/2018

8/27/2018
More
hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya ta ce yanzu haka rabin makarantun duniya basu da tsaftatacin ruwan sha, da kuma bandaki, tare da wajen wanke hannu.

Duration:00:15:45

Ra'ayoyin masu saurare kan barka da Sallah a Nijar - 22/08/2018

8/21/2018
More
A yau ne al'umar musulmi suka gudanar da shagulgulan sallar layya a kasar jamhuriyar Nijer. Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya baiwa wasu daga cikin masu saurarenmu damar isar da barka da sallarsu ga yan uwa da abukan arziki a kasar, tare da Zainab Ibrahim.

Ra'ayoyin masu saurare kan cimma yarjejeniyar sulhu ta karshe tsakanin Salva Kiir da Riek Machar - 06/08/2018

8/5/2018
More
Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan lokaci, ya bada damar tattaunawa ne kan bangarorin siyasar da ba sa ga maciji da juna a Sudan ta Kudu, a karo na karshe, sun sanya hannu a kan yarjejeniyar raba madafun iko a kasar Sudan, wanda ake sa ran za ta haifar da kafa Gwamnatin hadin kai, kowane bangare kuma zai bada gudumawar Ministoci da ‘yan Majalisu.

Duration:00:15:12

Ra'ayoyin masu saurare kan dawowar tsohon shugaban 'yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo gida - 02/08/2018

8/1/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare tare da Zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin baki kan dawowar madugun 'yan tawayen Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Jean Perri Bembe gida kinshasa a jiya Laraba.

Duration:00:14:51

Ra'ayoyin masu saurare kan ficewar Bukola Saraki daga APC - 02/08/2018

8/1/2018
More
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare tare da Zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin baki kan ficewar shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki daga Jam'iyya mai mulki ta APC zuwa tsohuwar Jam'iyyarsa ta PDP.

Duration:00:16:05

Ra'ayoyin masu saurare kan abin da ke ci muku tuwo a kwarya - 27/07/2018

7/26/2018
More
Shirin Ra'ayoyin masu saurare tare da Zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin baki kan duk wani abu da ke ci muku tuwo a kwarya ko kuma yabawa ko jinjina kan wani batu koma yin kira ga shugabanni kan wasu fannonin rayuwa.

Duration:00:15:38

Ra'ayoyin masu saurare kan gargadin fuskantar matsala a zaben Najeriya na 2019 daga wasu kungiyoyin Amurka - 23/07/2018

7/22/2018
More
Shirin Ra'ayoyin masu saurare tare da Zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin baki kan gargadin da wasu kungiyoyin kare Dimokradiyya daga Amurka suka yi game da yiwuwar fuskantar matsala a babban zaben Najeriya na 2019 matukar ba a shawo kan rikicin Makiyaya da Manoma da kuma na Boko haram ba.

Duration:00:15:42

Ra'ayoyin masu saurare kan abin da ke ci muku tuwo a Kwarya - 20/07/2018

7/19/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare tare da zainab Ibrahim a yau Juma'a ya baku damar tofa albarkacin bakinku kan duk wani abu da ke ci muku tuwa a kwarya.

Duration:00:15:10

Ra'ayoyin masu saurare kan badakalar Inshorar lafiya a Najeriya - 19/07/2018

7/18/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare ya baku damar tofa albarkacin baki kan ikirarin da hukumar da ke kula da Inshorar lafiya a Najeriya ta yi na cewa ta gano yadda wasu shugabannin hukumar da hadin bakin wasu bankuna suka wawashe dukiyar al'umma da ta kai dala biliyan 720.

Duration:00:15:08

Ra'ayoyin masu saurare kan nasarar Faransa a gasar cin kofin duniya - 16/07/2018

7/15/2018
More
Shirin a yau ya baku damar tofa albarkacin bakinku kan nasarar Faransa a gasar con kofin duniya.

Duration:00:15:26

Ra'ayoyin masu saurare kan bata-garin 'yan siyasa da ke rura wutar rikici a Najeriya - 10/07/2018

7/9/2018
More
Gwamnatin Najeriya ta bayyana sauyin yanayi da wasu bata garin yan siyasa da kuma wadanda ke dawowa daga Libya a matsayin wadanda ke tinzira rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnatin tace yanzu haka tana da shaidun dake nuna mata wadannan gurbatattun yan siyasar.

Duration:00:15:42

Ra'ayoyin masu saurare kan ziyarar Macron a Najeriya - 04/07/2018

7/3/2018
More
Shirin Jin Ra'ayoyin Masu Saurare na wannan rana ya tattauna ne game da ziyarar shugaban Faransa Emmanuel Macron a Najeriya, in da ya yi alkawarin tallafa wa kasar a fannoni da dama da suka hada ...

Duration:00:03:52

Ra'ayoyin masu saurare kan abin da ke ci muku tuwo a kwarya - 29/06/2018

6/28/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare tare da Zainab Ibrahim a yau juma'a ya baku damar tofa albarkacin baki kan duk wani abu da ke ci muku tuwo a kwarya.

Duration:00:15:29

Ra'ayoyin masu saurare kan zaman sulhun Riek Machar da Salva Kirr - 28/06/2018

6/27/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare tare da Ahmed Abba ya baku damar tofa albarkacin baki kan zaman tattaunawar Salva Kiir da Riek Machar wadanda ke matsayin shugaba da mataimakin Sudan ta kudu bayan karbar 'yancin kasar kafin barkewar rikici tsakaninsu da ya juye zuwa rikicin kabilanci.

Duration:00:15:55

Ra'ayoyin masu saurare kan ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi - 26/06/2018

6/25/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare a yau Talata tare da Ahmed Abba ya baku damar tofa albarkacin baki kan ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da majalisar dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 26 ga watan Yuni don gudanarwa.

Duration:00:15:15

Ra'ayoyin masu saurare kan sanya hannun shugaban Najeriya a kasafin kudin kasar na 2018 - 21/06/2018

6/20/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare na yau Alhamis tare da Zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin baki yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin 2018, dama yadda wasu mambobin majalisun kasar suka kauracewa zaman na jiya.

Duration:00:15:11

Ra'ayoyin masu saurare kan takaddamar da ke tsakanin kasashen Turai game da 'yan cirani - 18/06/2018

6/17/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare a wannan karon tare da Ahmed Abba ya baku damar tofa albarkacin bakinku kan jirgin 'yan ci rani da ya sha yawo a gabar tekunan kasashen Turai kafin a samu kasar da ta karbe shi dama takaddamar da ke tsakanin kasashen na Turai game da 'Yan ciranin.

Duration:00:15:10

Ra'ayoyin masu saurare kan yadda aka gudanar da bikin sallah a Nijar - 14/06/2018

6/13/2018
More
Shirin ra'ayoyin masu saurare a yau Alhamis tare da Zainab Ibrahim ya baku damar yin tsokaci kan yadda Nijar ta gudanar da sallar Idi a yau kwana guda gabanin Najeriya. ayi saurare lafiya.

Duration:00:15:05

Ra'ayoyin masu saurare kan karramawar da Buhari ya yiwa Abiola game da ranar 12 ga watan Yuni - 13/06/2018

6/12/2018
More
Ra'ayoyin masu saurare na yau Laraba tare da zainab Ibrahim ya baku damar tofa albarkacin bakinku kan karramar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yiwa Abiola ta hanyar mayar da 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Dimokradiyyar Najeriyar.

Duration:00:15:58