Daga Laraba-logo

Daga Laraba

News & Politics Podcasts

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Location:

Nigeria

Description:

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Language:

Hausa

Contact:

08028788121


Episodes

Hakikanin Abin Da Ya Sa Aka Ki Sakin Naira

3/15/2023
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya leka banki da kasuwa kuma ya gano yadda jama’a ke fama da rashin kudi, ga shi kuma wasu ’yan kasuwa sam ba sa karbar tsohuwar Naira, sai sabuwa ko taransfa. Ko yaushe za’a sakar wa ’yan Najeriya Naira? Saurari Daga Laraba domin jin amsar wannan tambaya, dama wadansu masu alaka. Za ku so karanta wadannan

Duration:00:29:58

Wane Ne Bola Ahmed Tinubu? Bayani Daga Dattawan Legas

3/8/2023
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya yi wasu tambayoyi masu kalubale ga shugaban kasar Najeriya mai jiran gado game da lafiyarsa, da kuma kaifin basirarsa. Shin Bola Ahmed Tinubu zai iya tafiyar da harkokin mulkin Najeriya fiye da Muhamadu Buhari? Ku surari shirin Daga Laraba na wannan mako ku ji amsoshin duka tambayoyin namu.

Duration:00:29:01

Ba-zatan da Zaben 2023 Ya Zo Da shi

3/1/2023
Ku biyo shirin Daga Laraba na wannan karo ku ji yadda sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya na shekarar 2023 ya zo da sabon salon da watakila ba a taba ganin irinsa a wannan zamanin ba. A cikin shirin, za ku ji yadda gwamnoni masu ci suka sha kasa a yunkurinsu na zuwa Majalisar Dattawa.

Duration:00:31:02

Anya INEC Ta Shirya Wa Zaben 2023?

2/22/2023
Ranar Asabar 25 ga Watan Fabrairun da muke ciki ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayyar Najeriya. Shin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya gudanar da wannan gagarumin aiki? Shirin Daga Laraba ya leka lungu da sako a Najeriya domin sanin matakin shirin hukumar zaben da kai.

Duration:00:29:54

Wa Zai Lashe Zaben Shugaban Najeriya?

2/15/2023
Nan da kwana tara ’yan Najeriya za su zabi sabon shugaban da zai mulke su na tsawon shekaru hudu idan Allah ya yarda. Bisa la’akari da yadda yakin neman zabe ke gudana, wane ne cikin ’yan takarar ke da alamun nasara a zaben na mako mai zuwa? Shirin Daga Laraba ya tattauna da kwamitin yakin neman zaben manyan ’yan takarar da ake sa ran daya daga cikinsu zai zamaz zababben shugaban kasar Najeriya, inda kowannensu ya bayyana yadda yake kallon nasara da kuma kalubalen da ke gabansu. A yi...

Duration:00:30:46

Abin Da Ya Sa 'Yan Mata Ke Tallata Kansu a ‘Soshiyal Midiya'

2/8/2023
Sabuwar dabi’ar neman miji ta kafofin sada zumunta da ’yan mata ke yi na neman zama ruwan dare. Bisa al’adar bahaushe dai, namiji ne ke ganin mace ya ce yana so; To amma sai ga shi ’yan mata sun dukufa tallata kansu ga mai so a kafofin sada zumunta. Shin me ke faruw ne? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wasu ’yan mata kan abin da ke sa su dora hotunansu a kafofin sada zumunta don neman miji; mun kuma ji ta bakin samari kan yadda suke kallon matan da ke yin hakan.

Duration:00:30:08

Dalilin Da Mutane Ke Karya

2/1/2023
A farko babu wanda ke yarda yana dan taba karya lokaci bayan lokaci. Amma idan aka dan matsa da bincike sai a samu jama’a da dama na dan tabawa. Ko mene ne ya sa mutane ke yin karya? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadansu da suka yarda suna yin karya, sun fadi dalilansu, mun kuma ji ta bakin masana kan dalilin yin karya da kuma hukuncinta.

Duration:00:30:04

Yadda Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Wasu ’Yan Najeriya Suka Rage Cin Abinci

1/25/2023
Matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ta tilasta wa 'yan Najeriya sauya yadda suke rayuwa. Shin kun san irin halin da jama'a ke ciki, kawo yanzu? Shirin Daga Laraba ya binciko hakikanin halin da ake ciki, ya kuma tuntubi dalilai.

Duration:00:29:59

Alakar ’yan aiki da iyayen gidansu: A ina gizo ke saka?

1/18/2023
Batun alaka tsakanin ’yan aiki da iyayen gidansu ya jima yana daukar hankali a fagen musayar ra'ayi. Shin tsakanin ’yan aikin da masu daukarsu, wa ke da alhakin abin da ke faruwa? Shirin Daga Laraba ya kutsa lungu da sako, ya zakulo ’yan aiki ya kuma ji ta bakin masu daukar aikin.

Duration:00:27:15

Dalilin Da Maza Ke Shakkar Auren Mata 'Yan Boko

1/10/2023
Muhawara kan abin da ke sa maza tsoron matan da suka yi karatun boko mai zurfi ko masu dukiya, batu ne da ya jima yana daukar hankalin jama’a da dama. Shin ko matan da suka yi karatun boko mai zurfi sun san dalilan da maza ke tsoronsu? Shirin Daga Laraba ya binciko wadan nan dalilai, ya kuma baje su a gadon fida, inda masana suka fede biri har wutsiya.

Duration:00:29:54

Yadda Yaudara Ta Zamo Ruwan Dare A Fagen Soyayya

1/4/2023
A kwankin baya mun kawo muku shiri na musamman akan yadda ake aure da ciki a wannan zamani. Wannan karon, shirin ya dubi yadda yaudara ta zamo ruwan dare a tsakanin masu shirin aure. Shin kunsan yadda yaudara ta zamo rigar ado a wannan zamani? Shirin Daga Laraba na tafe da bayanai masu ratsa zuciya, da kuma mafita kan yaudara a fagen soyayya.

Duration:00:29:55

Yadda Son Mata Da Dukiya Ke Raba Zumunci

12/28/2022
Zumunci wani jigo ne a tsarin rayuwar malam Bahaushe a shekarun baya, amma yanzu yana neman zama tarihi. Shin yaya aka yi yanzu zumunci ke neman zama labari a tsakanin al’umma? Shirin Daga Laraba na kunshe da bayanai. A yi sauraro lafiya.

Duration:00:29:16

Yadda Ake Aure Da Ciki A Kasar Hausa

12/21/2022
Shin idan ka gano cewa da cikin wani amaryarka ta shigo gidanka wane mataki za ka dauka? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya bankado al’ada yin aure da juna biyu a Arewacin Najeriya. Shin da sanin angwaye ake daura musu aure da mata masu ciki? Gyara zama domin jin yadda ta kaya tsakanin wadansu angwaye da amarensu suka zo musu da cikin wasu.

Duration:00:29:19

Yadda Talla Ke Bata Rayuwar Yaran Arewa

12/14/2022
Matsalar yawon talla ta dade tana ci wa al’ummar Arewacin Najeriya tuwo a kwarya. Me ya sa aka fi dora wa ’yan mata talla ta kasar Hausa kuma tsakanin amfani da illolin talla wanne ne a gaba? Shirin Daga Laraba ya dubi maganar talla da idon basira, don neman mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomi da masana a fannin ilimin addini da na duniya.

Duration:00:30:46

Jabun Kayayyaki: Ina Hukumar SON Ta Shiga Ne?

12/7/2022
Shin me ya sa kayayyaki marasa inganci suka zama ruwan dare a Najeriya? Wani lokacin kayayyaki na jabu ko lalatattu da ake sarrafawa ko sayar wa ’yan Najeriya na hallaka da dama a cikinsu. Me hukumar da ke kula da ingancin kayayyaki ke yi don hana kawo wa ’yan Najeriya kayayyaki marasa inganci? Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin wainar da ake toyawa.

Duration:00:30:36

Yadda Zubar Da Ciki Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya

11/30/2022
Zubar da ciki al'amari ne mai ba da tsoro saboda hadarinsa da kuma alhakin da ake iya dauka idan an yi ba bisa ka’ida ba. Shin ko mene ne dalilin da zubar da ciki ya zama ruwan dare a tsakani ’yan mata da matan aure a Najeriya? Saurari cikakken shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin yadda matan aure da ’yan mata suka maida zubar da ciki abin wasa.

Duration:00:29:55

Maganin Karfin Maza: Gyara Ko Janyo Ciwo?

11/23/2022
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya mayar da hankali ne a kan maganin karfin maza, amfaninsa, illolinsa da kuma shawarwarin masana a kai. Wannan kari ne a kan shiri na musamman da muka kawo muku a baya kan maganin mata, wanad aka fi sani da kayan mata da yadda ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman a Arewacin Najeriya.

Duration:00:29:56

Yadda Iyaye Ke Lalata Da ’Ya’yan Cikinsu

11/16/2022
Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya dubi yadda matsalar lalata tsakanin iyaye da ’ya’yansu ko tsakanin yayyu da kanne ta zama ruwan dare ne. Mun tattaro bayanai masu nuna yadda kwamacalar take kara kamari a wannan zamani.

Duration:00:29:45

Yadda Yi Wa Kananan Yara Fyade Ya Yadu A Arewacin Najeriya

11/9/2022
Me ya sa ake yawan samun mutane masu manyan shekaru da ke afka wa kananan yara mata ko mazayarinya ko karamin yaro? Shin wane dalili ke sa kawo yawaitar wannan kazamar dabi’a ta lalata da kananan yara? Shirin Daga Laraba ya dubi yadda wannan matsala ta zama ruwan dare, musamman a Arewacin Najeriya. A yi sauraro lafiya.

Duration:00:30:23

Abin da kishi ke sa maza aikatawa

11/2/2022
Duk lokacin da aka ambaci zafin kishi, to da dama mata ke zuwa zukatan jama’a. Shin yaya maza ke kishi, kuma me suke iya aikatawa saboda tsananin kishi? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da masu ruwa da tsaki game da tsananin kishin maza, abin da yake iya sa su da kuma yadda ya kamata a yi kishin.

Duration:00:29:58