Daga Laraba-logo

Daga Laraba

News & Politics Podcasts

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Location:

Nigeria

Description:

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Language:

Hausa

Contact:

08028788121


Episodes
Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Me Ya Kamata A Yi Lokacin Komawar Yara Makaranta?

9/4/2024
A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu. Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a Najeriya? Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan wannan batu na komawa makanta bayan hutun dogon zango.

Duración:00:21:51

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Muhimmancin Al'adar Ciyayya.

8/28/2024
Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum. Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare. Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan muhimmancin wannan Al'ada, musamman la'akari da irin halin da ake ciki yanzu a Najeriya.

Duración:00:26:22

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Me Ya Kamata A Yi Wa Mutanen Da Rikicin Ta’addanci Ya Rutsa Da Su?

8/21/2024
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su. A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.

Duración:00:26:09

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Abin Da Ke Faruwa Da Bankunan Da Suka Haɗe Waje Guda

8/14/2024
A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna. A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya. To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi? Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi bayani kan abin da ke faruwa a duk lokacin da bankuna suka yi maja a waje da juna.

Duración:00:23:09

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Yadda Za Ku Gane Shafukan Tallafin Gwamnati Na Bogi

8/7/2024
Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma. Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan intanet na tallafin gwamnati na bogi da na gaske.

Duración:00:23:53

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Abin Da Gwamnati Za Ta Yi Idan Tana Son Hana Zanga-Zanga

7/31/2024
Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka. Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma. Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.

Duración:00:27:41

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Dabarun Kauce Wa Dagulewar Lissafi Sakamakon Ruwan Sama

7/24/2024
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya. Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali. Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.

Duración:00:23:21

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Ko Tallafin Shinkafar Gwamnati Zai Magance Damuwar Talakan Najeriya?

7/17/2024
Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi. A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri. Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya.

Duración:00:24:56

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Matakan Kauce Wa Hadarin Ambaliyar Ruwa

7/10/2024
Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa. A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine. Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.

Duración:00:29:48

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Digiri Ko Sana’a - Wanne Ya Fi Muhimmanci?

7/3/2024
Ana ci gaba da tafka muhawara a kan abin da ya kamata mutum ya fi bai wa muhimmanci a tsakanin digiri da sana’a. Shin wanne ne daga ciki mafi a'ala a rayuwar mutum? Shirin Daga Laraba zai yi muhawara a kan wannan batu.

Duración:00:29:50

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Shirin Gwamnonin Arewa Maso Yamma Na Magance Matsalar Tsaro

6/26/2024
Yayin da ake kammala taron yini biyu a kan matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, hankali ya karkata zuwa ga mataki na gaba. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda gwamnonin yankin suka shirya aiwatar da abin da aka cimma.

Duración:00:23:01

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Yadda Kanawa Suka Je Kallon Hawan Daushe A Zazzau

6/19/2024
Hawan Daushe al’ada ce ta sarakunan Kasar Hausa a lokacin bikin Sallah. A masarautar Zazzau a kan yi wannan hawa a ranar ukun Sallah da yamma, kuma yakan tara ‘yan Kallo daga wurare daban-daban ciki har da Kano. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda aka yi hawan na bana da yadda ya samo asali musamman a masarautar Zazzau.

Duración:00:28:40

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

‘Na Yi Nadamar Ajiye Aiki Saboda Tsohon Mijina’

6/12/2024
Yayin da wasu mazan suke kyale matansu su yi aiki, wasu kan yi kememe su ki bari nasu matan su yi. Shin barin matar aure ta yi aiki ne ya fi alheri ko hana ta? Wadanne dalilai kowanensu ke da su? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a cikin wannan lamari.

Duración:00:25:09

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Dalilin Da Maza Ba Su Son Likita Namiji Ya Duba Matansu

6/5/2024
A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci. Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.

Duración:00:28:54

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Ƙalubale Da Ci Gaban Dimokraɗiyar Najeriya Cikin Shekara 25

5/29/2024
Najeriya ta cika shekara 25 cikin tsarin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Ana kan tsari ne na shugaban kasa mai cikakken iko tun daga 1999 a ranar 29 ga watan mayu, duk da yake an sauya bikin wannann rana zuwa 12 ga watan Yuni. Toh shin wane irin ci gaba ko akasin haka aka samu cikin wadannan shekaru 25? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna kan wannan cikar Najeriya shekara 25 cikin mulkin dimokradiyya.

Duración:00:28:52

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Abin Da Ke Sa Fararen Hula Su Raina Sojoji

5/22/2024
Mu’amalar farar hula da sojoji a Najeriya ta mutuntuwa ce wadda zarar aka hangi soja a cikin gari jiki har karkarwa yake. Sai dai a ‘yan kwanakin nan a iya cewa yadda labarai ke yawan fita game da yadda fararen hula ke yin tsaurin ido wajen takalar sojoji da fada yana karuwa. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa fararen hula ke kokarin daga hannunsu kan jami’an tsaro musamman na soji.

Duración:00:23:12

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Aikin Hajji

5/15/2024
Yau Laraba rukunin farko na maniyyata Hajjin bana daga Najeriya za su tashi zuwa kasa mai tsarki Duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, akalla mutum sama da 50,000 ne ake sa ran za su sauke faralin daga Najeriya. Shin wane abu maniyyatan ya kamata su maida hankali a kai? NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga KudiDAGA LARABA: Dalilan Da Za A Hana ’yan kasa da shekara 18 shiga jami’aShirin Daga Laraba na wannan mako yana dauke da amsohin wadannan bayanai game maniyyata Hajjin bana.

Duración:00:29:49

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a

5/8/2024
Idan aka zagaya jami’o’i ana samun dalibai da dama wadanda ba su wuce shekara 15 ba a aji. A yanzu zamani ya sauya, abin ya zama Ruwan dare. Mai yiwuwa a lokacin da kuke makarantar firamare ko sakandare kun hadu da wadanda aka yiwa tsallaken aji, wato a bai wa dan aji 4 damar rubuta jarabawar kammala firamare ko kuma dan SS2 damar rubuta WAEC ya wuce jami’a Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta ce za a tabbatar da dokar hana duk wanda bai kai shekara 18 ba zuwa matakin gaba da sakandare. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi duba a kan wannan lamari.

Duración:00:23:35

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Muna Rayuwa A Cikin Ƙunci - Ma’aikatan Najeriya

5/1/2024
Yau ce ranar 1 ga watan Mayu da aka ware a Najeriya da wasu sassan duniya domin jinjina ga rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban kasa. Sai dai yayin da 'yan Najeriya da dama ke kuka da halin da aka shiga na ƙuncin rayuwa, ma'aikata na kan gaba wajen bayyana yadda suka ce suna tagayyara kuma aikin ba riba ta wani ɓangaren. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda rayuwar ma'aikata a Najeriya ke kasancewa da sauyin da ake fatan samu.

Duración:00:25:50

Pídele al anfitrión que permita compartir el control de reproducción

Me Ya Sa Kamfanonin Lantarki Suke Fifita ‘Yan ‘Band A’?

4/17/2024
Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne. Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata wani fanni.

Duración:00:25:53