Najeriya a Yau-logo

Najeriya a Yau

News & Politics Podcasts

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Location:

Nigeria

Description:

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Language:

Hausa

Contact:

09138933390


Episodes
Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya

4/30/2024
Karancin man fetur na neman tsayar da al'amura cak ga al'umma a wasu sassan Najeriya. Da dama sun ce lamarin ya shafe su kaitsaye kuma sakamakon haka suna dandana kudarsu. Shin yaushe wannan lamari zai zo karshe, musamman idan yi la’akari da cewa tun a Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya maganace matsalar? A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa sannan mu ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan yiwuwar samun mafita nan kusa.

Duration:00:14:37

Ask host to enable sharing for playback control

Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro

4/29/2024
Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar. Tafiyar gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare. Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin da taron zai yi wajen magance matsalar yankunan.

Duration:00:13:39

Ask host to enable sharing for playback control

Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba

4/26/2024
Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya? Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi. To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.

Duration:00:13:31

Ask host to enable sharing for playback control

Da Gaske Haƙa Rijiyoyin Burtsatse Na Haifar Da Matsala A Anguwanni?

4/25/2024
Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya. Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?

Duration:00:14:59

Ask host to enable sharing for playback control

Me Ya Sa Ake Ƙin Faɗa Wa Mata Wasu Abubuwa Idan Za Su Yi Aure?

4/24/2024
Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa. Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu. Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.

Duration:00:26:46

Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Tsananin Zafi Zai Iya Cutar Da Dalibai A Makarantu

4/23/2024
Hukumomi sun bayyana jihohin da za a samu matsanancin zafi a Najeriya. Lamarin ya zo daidai lokacin da makarantu ke komawa hutu, inda ake fargabar yiwuwar yaduwar cututtuka a azuzuwa masu cunkuso. Shin ta wace hanya makarantu za su kauce wa yaduwar cututtuka masu alaka da matsanancin zafi? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani

Duration:00:14:26

Ask host to enable sharing for playback control

Rawar Da NNPP Ke Takawa A Dambarwar Dakatar Da Ganduje

4/22/2024
Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can. Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.

Duration:00:15:26

Ask host to enable sharing for playback control

Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri Ɗaya

4/19/2024
Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya. Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka? Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.

Duration:00:14:57

Ask host to enable sharing for playback control

Me Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Ƙi Karya Farashi Duk Da Karyewar Dala?

4/18/2024
Ana ta murnar dalar Amurka na karyewa watakila a samu saukin kayan masarufi. Sai dai a ganin wasu yadda ‘yan kasuwa suke azamar tsawwala kudi idan ta tashi ba su yi hakan ba a yayin da take saukowa. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilin da ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su sauke farashin kayayyaki.

Duration:00:15:15

Ask host to enable sharing for playback control

Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A Jam’iyar APC?

4/16/2024
An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba. Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa. To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.

Duration:00:14:58

Ask host to enable sharing for playback control

Albashin Da Ya Kamata A Riƙa Biyan Ma’aikaci A Wannan Yanayi

4/15/2024
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ya sa komai ya sauya amma banda albashin ma’aikata. Akwai mahimman abubuwan da masu daukar albashi ba su iya yi saboda ma’aikatu da hukumomi sun kasa matsawa da albashinsu gaba. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da ya kamata mutum ya fara dubawa ta fannin albashi kafin karbar aiki.

Duration:00:12:03

Ask host to enable sharing for playback control

Shin Ya Dace Mace Ta Fara Sitta-Shawwal Kafin Biyan Bashin Ramadan?

4/12/2024
Wane lokaci ya fi dacewa mutum ya fara azumin sitta-shawwal? Ana yawan shiga rudani kan hakan, da kuma tunanin cewa mace wadda ake binta bashin azumin Ramadan ko ya kamata ta dauki azumin kafin biyan bashi? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani da wasu batutuwan da ya kamata ku sani game da azumin na kwanaki shidan bayan karamar Sallah.

Duration:00:13:02

Ask host to enable sharing for playback control

‘Da Ƙyar Muka Iya Cefanen Sallah Bayan An Sauko Idi’

4/11/2024
Matsin rayuwa yana daga cikin abin da ya hana mutane da dama yin shagali da wannan karamar Sallah. Wasu ma basu iya yin cefanen Sallah na abincin da za a ci ballantana sabbin dinkuna. Shirin Najeriya a Yau ya zagay wasu jihohu domin yadda mutane suka yi Sallah cikin matsin rayuwa.

Duration:00:14:07

Ask host to enable sharing for playback control

Wani Tela Ya Tsere Saboda Rashin Gama Ɗinkunan Sallah

4/9/2024
Teloli iyayen haɗa gwarama! An saba kai ruwa rana a kowace Sallah idan teloli suka sha ta fi karfinsu. Sai dai ba saban ba, wani telan da muka zanta da shi ya ce ya kammala dinkunan da ya karba kakaf yayin da wani ya tsere ya bar masu kaya da wayyo! Shin wadanne dabaru ya kamata tela ya yi amfani da su wajen ganin ya sallami kowa? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.

Duration:00:13:43

Ask host to enable sharing for playback control

Mutanen Da Aka Haramtawa Cin Zakkar Kono

4/8/2024
Shin a wane lokaci aka yi umarnin fitar za Zakkar Fidda Kai? Malamai sun ce wannan Zakka tana da matukar mahimmanci ga masu hali kuma akwai lokacin da aka kayyade a fitar da ita; in ba haka ba kuma ta zama sadaka. Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan fidda Zakatul-Fitr da mutanen da aka haramtawa cin ta.

Duration:00:13:13

Ask host to enable sharing for playback control

Me Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Tsarin Raba Wutar Lantarki?

4/5/2024
Tun bayan da aka kara kudin wutar lantarki mutane ke ta korafi game da yadda aka rarraba tsarin. Amma har yanzu wasu na cewa ba su fahimci yadda tsarin yake tafiya ba da kuma yadda lamarin ke neman shafar rayuwarsu matuƙa. Shirin Najeriya a Yau ya tattaun kan abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon tsarin rabon lantarkin.

Duration:00:15:29

Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Za Ku Gane Daren Lailatul-Ƙadri Cikin Sauƙi

4/4/2024
Akwai abubuwa na musamman da aka fi son a roƙa a irin wannan dare. Yawanci an fi maida hankali a ranakun wutiri daga 25 zuwa 29, duk da yake malamai na ba da shawarar a yi ibada sosai a dukkanin ranakun goman karshe. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da malamai gameda alamomin gane daren lailatul-ƙadri da abin da aka fi son bawa ya roƙa a ciki.

Duration:00:14:28

Ask host to enable sharing for playback control

Matakan Kariya Daga Ɓata Gari A Lokacin Zuwa Tahajjud

4/2/2024
Yanayin tsaro na jefa fargaba a zukatan wasu Musulmi da ke zuwa sallar dare ta Tahajjud. Wasu ɓata gari kan yi amfani da wannan damar da mutane ke fita tsakar dare domin aikata musu abin da bai dace ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba wasu matakai na tsaro da za ku dauka domin kare kanku daga fadawa matsala.

Duration:00:13:41

Ask host to enable sharing for playback control

Mutuwar Zuciya Ce Ta Jefa Matasa Harkar Kirifto

4/1/2024
Shin a ganinku me ya sa matasa 'yan soshiyal midiya suka dukufa a harkar nan ta kirifto musamman 'mining' ? A yanzu haka da dama ne cikin matasan ke jiran ta fashe domin su kudance, sai dai akwai masu yi wa irin wadannan matasa kallon masu raunin zuciya. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da masu harkar mining da kuma masana kirifto kan abin da ya kamata ku sani kafin ku fara hakowa.

Duration:00:15:45

Ask host to enable sharing for playback control

Illolin Yawaita Amfani Da Soshiyal Midiya A Ramadan

3/29/2024
Yawan amfani da Soshiyal Midiya na haifar da gane-ganen abubuwan da ba su kamata ba. A lokacin Ramadaan yana da kyau mutum ya yi kokarin kaucewa duk wani abin da zai raunana mishi azumi. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da zai faru da ku idan kuka yawaita amfani a da soshiyal midiya a lokacin Ramadan.

Duration:00:12:51