Najeriya a Yau-logo

Najeriya a Yau

News & Politics Podcasts

Duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, da tsokaci maii warkarwa, a kan batutuwan da ke jan hankali a labaran yau da kullum.

Duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, da tsokaci maii warkarwa, a kan batutuwan da ke jan hankali a labaran yau da kullum.

Location:

Nigeria

Description:

Duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, da tsokaci maii warkarwa, a kan batutuwan da ke jan hankali a labaran yau da kullum.

Language:

Hausa

Contact:

09138933390


Episodes

Shekara Guda Da Fara Rediyon Aminiya Na Tafi Da Gidan ka (podcast); Yadda Muka Faro

5/19/2022
Yau rediyon Aminiya na tafi da gidan ka (podcast) ke cika shekara guda da fara yada shirye-shiye. Daga ranar 19 ga watan Mayun 2021 da muka faro zuwa yau, mun wallafa shirin Najeriya A Yau sau 171 mun kuma wallafa shirin Daga Laraba guda 53. Shirin namu na yau ya yi waiwaye ne kan yadda muka faro da kuma ra'ayoyin wadansu masu sauraro kan shirye-shiryen mu.

Duration:00:15:00

Wuraren Da Rashin Tsaro Zai Hana Noma Bana

5/17/2022
Manoman da 'yan bindiga suka kora daga gidajensu na fama da zullumin yadda rayuwarsu zata kasance sakamakon rashin iya wata sana'a bayan noma; wanda a yanzu kuma babu halin yi. Wace barazana ke fuskantar Najeriya a sakamakon rashin samun wadataccen noma da za a yi?

Duration:00:14:50

Matsayin Daukar Doka A Hannu A Mahangar Shari’a

5/16/2022
Mene ne kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan wanda aka fusata shi ya dauki doka a hannunsa? Tun bayan abin da ya faru na zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a Sakkwato da daukar matakin da matasan Musulmi suka yi na halaka wacce ta yi batancin nan take, jama’a ke ta musayar ra’ayi kan matsayin shari’a kan wannan batu. Wakilinmu a Jihar Sakkwato ya fada mana halin da jihar ke ciki, mun kuma ji ta bakin wani mai fashin baki kan dokokin kasa kan abin da ya faru.

Duration:00:14:47

Yadda Dokar Zabe Ta Kawar Da ’Yan Fadar Buhari

5/13/2022
Shin akwai lokacin da zababbun shugabanni a Najeriya za su sauka daga kujerunsu idan suna son tsayawa takarar zabe? Kawo yanzu dai, dokar zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a watan Fabrairu ta wajabta mishi sauke ’yan fadarsa masu niyyar shiga zabe. Shin wane tasiri wannan sauyi da sabuwar dokar zai yi ga dimokuradiyyar kasar? Wadannan da ma wasu batutuwan da suka shafi dokar zaben Najeriya ne batun da shirin namu ya mayar da hankali a kai. A yi sauraro lafiya.

Duration:00:15:09

Hatsarin Da ASUU Ke Neman Jafa Najeriya A Ciki

5/12/2022
Tunda daliban Jami'oi mallakar Gwamnatin Tarayya da na jihohi suka dawo gida sakamakon yajin aikin ASUU, masu nazari suka shiga bibiyar kalubalen da zaman wadan nan dalibai zai janyowa Najeriya. Shin wane hali yajin aikin ASUU ya jefa daliban kuma wane tasiri hakan zai yi a kan kasar?

Duration:00:13:13

Yadda Sauyin Yanayi Zai Shafi Daminar Bana

5/10/2022
Alamu sun fara nuna yadda sauyin yanayi zai shafi daminar bana, bayan hasashen hukumomin Najeriya suka yi kan ruwan sama da kuma katsewarsa a farkon daminar. Ana ciki haka sai ga wata guguwa mai karfin gaske da ta shafi jihohin Adamawa da Katsina a makon jiya. Mun tattauna da Hukumar lura da yanayi ta Najeriya da kuma masanin kimiyyar noma domin jin yadda za a tunkari wadannan kalubalenen.

Duration:00:15:02

APC A Idon 'Yan Najeriya Bayan Tara Fiye Da N20bn

5/9/2022
Tun bayan bayyana kudin fom din takarar jam’iyyar APC ’yan Najeriya suke zura ido domin ganin wadanda za su saya. Rahotanni sun bayyana cewa kudaden da jam’iyyar ta tara kawo yanzu, sun sa yawancin ’yan Najeriya sun saki baki saboda mamaki, lura da yadda APC din take yawan ambatar yaki da cin hanci. ’Yan Najeriya da masu sharhi sun bayyana wa shirin Najeriya A Yau irin kallon da suke yi wa jam’iyyar, da kuma makomar matakin jam’iyyar na sayar da fom din takararta a kan farashin da ya zarce...

Duration:00:15:00

Bankwana Da Ramadan, Maraba Da Shawwa

4/29/2022
A lokacin da watan Ramadan ya taho karewa, ta wace hanya za a kammala ibadun da suka rage domin neman yardar Allah? Wane ne ya kamata ya fitar da Zakkar Kono da ake bayarwa a karshen azumin Ramadan, yaya ake fitarwa kuma me ake yi? Malamai sun yi wa shirin Najeriya A Yau gamsasshen bayanai kan wannan batu da kuma sauran ibadun da ake so Musulmi ya gabatar a watan Karamar Sallah. A yi sauraro lafiya.

Duration:00:14:46

Za A Kai Harin Bom Wuraren Ibada_DSS

4/28/2022
Kwana 30 da harin Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja da ya yi sanadiyyar satar mutane da dama, Hukumar DSS ta yi hasashen sabbin hare-hare a wuraren ibada da na shakatawa. wane shiri gwamanti da limamai da fastoci ke yi da samun wannan labari daga hukumar DSS?

Duration:00:15:58

Yadda Bara Ta Shigo Karatun Allo

4/26/2022
Batun yawon bara da almajirai ke yi a birane da ƙauyuka domin neman abinci da sutura ya ɗauki hankalin mutane a Najeriya. Wai shin bara wani yanki ne na karatun Allo ko kuma saɗaɗowa al'adar ta yi har aka wayi gari ba a iya raba karatun Allo da yawon bara? Yaushe aka fara yawon bara a tsarin karatun Allo? Shin kuskure ne ko kuma daidai ne? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da amsoshin waɗannan tambayoyi dama ƙarin bayani.

Duration:00:15:08

Dalilanda Jiragen Sojan Najeriya Ke Yawan Yin Hatsari

4/25/2022
Daga shekarar 2015 zuwa 2022 jiragen Sojan Najeriya 11 sunyi hatsari, wanda sanadiyyar wannan hatsari anyi asarar rayuka da dukiya mai yawan gaske. ko mene ne ke sa jiragen sojan Najeriya yawan faduwa, in ya fado wace irin asara ake tafkawa, shin an kamo hanyar gyara kuwa? Akwai amsoshin wadannan da ma wadansu tambayoyin a shirin namu na yau.

Duration:00:18:01

Yadda Za A Ribaci Kwanaki Goma Na Karshen Ramadan

4/22/2022
Musulmin duniya baki daya na hankoron dacewa da falalar kwanaki goman karshe na watan azumin Ramadan. Sanin cewa a cikin wadannan kwanaki goma na karshen Ramadan ake riskan daren “Lailatul Kadari”, kirdadon wannan dare na sa Musulmin dagewa da ayyukan ibada. Wadanne ibadu aka fi son a yawaita a wadannan kwanaki masu alfarma?

Duration:00:15:08

Yadda Tsadar Takardar Takara Za Ta Shafi Zaben 2023

4/21/2022
Kudin takardun takarar babban zaben 2023 ya ninku akalla sau biyu a kan na zaben 2019. Daga Jam’iyyar APC mai mulki zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP har da sabuwar jam'iyyar NNPP, abin samma-kal. Mene ne dalili Ko me ya sa hakan faruwa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani

Duration:00:13:05

Yadda Aminu Kano Ya Fara Daukar Mace Mataimakiyar Dan Takarar Shugaban Kasa

4/19/2022
Bayan shekara 38 da barin duniya, ’yan Najeriya na ci gaba da tunawa da Malam Aminu Kano a bangarori da dama. Jama’a da dama na kallon Malam Aminu Kano a matsayin wanda ya sauya akalar siyasar Najeriya ta hanyar zama mutum na farko da ya zabi zabi mace a matsayin ’yar takararsa ta mataimakin shugaban kasa. Shin kawo yanzu, burin Malam din na ganin an dama da kowa da kowa a fagen siyasa ya cika kuwa?

Duration:00:14:32

Abin Da Ya Sa Aka Yafe Wa Dariye Da Jolly Nyame

4/18/2022
Yafe wa tsohon Gwamnan Taraba Jolly Nyame da na Filato Joshua Dariye ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Abin da da dama ke kallo shi ne irin kudaden da wadannan bayin Allah suka salwantar a lokacin da suke kan karagar mulki. Mene ne abin da doka ta ce danagne da yafe wa wanda ya zalunci al’umma da dama?

Duration:00:14:59

Karshen Tashe A Kasar Hausa

4/15/2022
Goman tsakiya na watan Ramadan lokaci ne da ake fatan gani a kasar Hausa, saboda ayyukan ibada da ake yawaitawa da kuma wasan tashe da ake nishadantar da jama’a a unguwanni da sauran wurare. Mene ne tarihin tashe da amfaninsa kuma ya aka yi ya rasa martabarsa da kimarsa a kasar Hausa?

Duration:00:15:09

Yadda ’Yan Bindiga Ke Sheke Ayarsu A Filato Da Taraba

4/14/2022
’Yan bindiga sun samu gangarar wadansu yankunan jihohin Taraba da Filato ta yadda duk lokacin da su ka ga dama suke zuwa su kaddamar da hari kan mutanen kauyuka daban-daban daga lokaci zuwa lokaci. Me ya kamata a yi kuma su wa ya kamata su taimaki wadannan mutane?

Duration:00:14:35

2023: Yadda Tinubu Ya Karbi Batun Takarar Osibanjo

4/12/2022
Hankalin ’yan Najeriya ya koma kan yadda Uban Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ke neman takarar shugaban kasa ya ji da fitowar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, takarar kujerar. Da wace fuska Tinubun ya karbi aniyar ta Osibanjo, wanda ake kallo a matsayin yaron gidansa? Shin wuyan Osinbajo ya kai yanka? Wadanne kalubale takarar tasa take tattare da su? Sannan tsakanin shi da Tinubu wa zai dagula wa wani lissafi? Shirin Najeriya A Yau na wannan na tafe gamsassun...

Duration:00:13:46

Yadda Ruwan Sha Ke Neman Gagaran Talakan Kano, Katsina da Jos

4/11/2022
Jama'ar Kano, Katsina da Jos na fama da rashin ruwan sha da na ayyukan yau da kullum a cikin gida. Hakan ya jefa da yawa cikin mawiyacin hali. A cikin shirin za ku ji yadda mutane ke barin gidajensu cikin dare domin neman ruwansha da na ayyuka. Shirin Najeriya A Yau ya bankado inda gizo ke saka

Duration:00:15:04

Hukuncin Wanke Bakin Mai Azumi Da Rana

4/7/2022
Jama'a da dama na tambayar halacci ko haramcin wanke baki da ashuwaki ko buroshi da man wankin baki da rana a wurin azumi. Wadansu na ganin bai halatta mai azumi ya wanke bakinsa da rana ba, wadansu kuma na ganin ya halatta. Shirin Najeriya A Yau ya binciko matsayar manzon Allah (S.A.W) akan wanke baki da rana a wurin mai azumi.

Duration:00:09:54