Najeriya a Yau-logo

Najeriya a Yau

News & Politics Podcasts

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Location:

Nigeria

Description:

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Language:

Hausa

Contact:

09138933390


Episodes
Ask host to enable sharing for playback control

Tasirin Auna Hauhawar Farashi A Rayuwar Talaka

5/21/2024
Wata kalma da ’yan Najeriya ke yawan ji ita ce ƙimar hauhawar farashi, wato ‘Inflation rate’ a turance. Sai dai kuma ba kowa ne ya fahimci abin da Kalmar take nufi ba, balle ya san yadda ake auna hauhawar farashin. Shin ta yaya yan kasa za su gane tasirin hakan a rayuwarsu ta yau da kullum? Shirin Najeriya a Yau zai yi kokarin amsa muku wadaannan tambayoyi. Ku biyo mu

Duration:00:14:11

Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Za Ku Ceto Yaron Da Ya Kamu Da Jijjiga

5/20/2024
Shin kun taba cin karo da yara masu jijjiga? wani yanayi ne da larurar kwakwalwa ko kasancewar guba a cikin jinni kan haifar wa manya, zazzabi mai tsanani kuma kan haifar wa yara. Yanayin kan sa yaro ya shiga yanayin sarkewar gabobin jiki da numfashi kamar dai mai farfadiya a wasu lokutan. Shirin Najeriya a Yau na dauke labarin wata matar da irin hakan ya faru ga 'yarta har ma da shawarwarin masana game da matakin da za ku iya dauka da alamomin da za ku iya gane mutum na cikin wannan yanayi.

Duration:00:14:00

Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Za Ka Ɗauki Mataki Idan Aka Ɓata Maka Suna Saboda Cin Bashi

5/17/2024
A wannan zamani da mutum zai iya samun bashi kaitsaye ta waya daga manhajoji daban-daban amma idan mutum ya kasa biya kamfanonin bada bashin kan aika sakonnin cin zarafi da barazana har ga ‘yan uwan wanda ya ci. Duk da gargadin da hukumomi mutane da dama na kukan ana ɓata musu suna, kuma an kasa kulle irin wadannan manhajoji kamar yadda aka ce. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan lamarin, da kuma matakin da mutum zai iya dauka idan kamfanin cin bashi suka bata masa suna.

Duration:00:15:29

Ask host to enable sharing for playback control

Dalilin Da Ba Za A Biya Wasu Ma’aikata Albashinsu Ba

5/16/2024
Gwamnatin tarayyar ta ce za a ɓullo da tsarin auna ƙwazon ma’aikata bisa mizani ta yadda dagewar ma’aikaci zai sa ya samu ƙarin girma ko albashin ma zai iya bambanta, wato dai iya kwazonka iya albashinka. Irin wannan yunkuri na gwamnatin tuni ma’aikata da ‘yan kwadago suka fara suka da tunanin wata manufa ce ta kauda hankali. Toh ko ta fannin shari’a hakan na da tasiri wajen hakkin ma’aikata? Shirin Najeriya a Yau ya tattauana kan wannan batu.

Duration:00:15:50

Ask host to enable sharing for playback control

Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga Kuɗi

5/14/2024
A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa wajen tsuga kudin haya. Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan yadda lamarin ke shafar rayuwar mutanen da suke zaune a gidajen haya.

Duration:00:15:30

Ask host to enable sharing for playback control

Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga

5/13/2024
Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga. Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan ta zargi gwamnatin Tarayya da hawa teburin shawarwari da ‘yan fashin daji ba da saninta ba. Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don mu duba abin da ya sa ake samun tankiya game da matsalar tsaro tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara.

Duration:00:14:10

Ask host to enable sharing for playback control

‘An Yafe Wa Masu PoS Biyan Harajin Yin Rijista Da CAC’

5/10/2024
Ga alama nan ba da dadewa ba yanayin sana’ar POS a kasar nan zai sauya. Babban Bankin Najeriya (CBN) ya wajabta wa masu wannan sana’a yin rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni da Kungiyoyi (CAC) zuwa nan da 7 ga watan Yulin 2024. To amma ya batun harajin da suke korafi a kai? Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don jin matsayar CAC game da biyan kudin.

Duration:00:15:51

Ask host to enable sharing for playback control

'Za Mu Ɗaure Duk Wanda Bai Yi Gwajin Jini Kafin Aure Ba'

5/9/2024
Sabuwar dokar da gwamnatin jihar Kano ta sanyawa hannu kan yin gwajin lafiya kafin aure na shan yabo da suka. A cewar gwamnatin, yawaitar yaduwar cututuka a tsakanin ma’aurata bayan aure shi ne makasudin yin wannan doka. Amma me ya sa za a daure wanda ya taka dokar tsawon shekara 5 ko tarar 500,000? Idan aka samu wanda ya taka dokar miji za a daure ko mata ko madaurin auren? Shirin Najeriya a Yau ya zanta da masu ruwa da tsaki da masana shari’a kan wannan doka.

Duration:00:14:28

Ask host to enable sharing for playback control

Abun Da Za A Fara Lura Kafin Shiga Tasi A Abuja

5/7/2024
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ne ya sa kowa ya koma neman kudi da mota don daukar fasinjan a Abuja. Sai dai hukumomi sun ce an dauki matakin hana duk wani mutum da bai cika ka'idojin yin tasi ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilan da suka sa hukumomi ke shirin tabbatar da halascin yin kabu-kabun ga masu zaman kansu ba tare da sun yi fentin ba.

Duration:00:14:34

Ask host to enable sharing for playback control

Ɓarkewar Cutar Ƙyanda: Sakaci Ko Annoba?

5/6/2024
A karshen shekarar 2023 ne dai, hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Cibiyar hana yaduwar cututtuka suka yi gargadi cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya. Sai ga shi kwatsam an samu rahotanni game da barkewar cutar a wasu yankunan Naijeriya har ta kashe wasu mutane da dama. Shirin Najeriya a Yau ya mayar da hankali ne kan cutar ta kyanda, da yadda za ku kare yaranku daga annobar.

Duration:00:14:58

Ask host to enable sharing for playback control

Dalilan Da Ake Yi Wa Mutum Kutse A Soshiyal Midiya

5/3/2024
Masu amfani da shafukan sada zumunta kan fada hannun masu dandantsa inda sukan yi kutse a shafin mutum har ya rasa iko da shi. Kwararru sun ce ana yi wa wasu hakan domin bata suna ko kuma neman kudi da damfara. Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da kwararru a fannin samar da matakan tsaro a soshiyal midiya game da dabarun inganta tsaron shafukanku.

Duration:00:14:37

Ask host to enable sharing for playback control

“Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...”

5/2/2024
Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno. Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya. Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke biyan irin wannan albashi da wasu suka ce bai taka kara ya karya ba.

Duration:00:15:34

Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya

4/30/2024
Karancin man fetur na neman tsayar da al'amura cak ga al'umma a wasu sassan Najeriya. Da dama sun ce lamarin ya shafe su kaitsaye kuma sakamakon haka suna dandana kudarsu. Shin yaushe wannan lamari zai zo karshe, musamman idan yi la’akari da cewa tun a Kamafanin Mai Na Kasa (NNPC) ya ce ya maganace matsalar? A shirin Najeriya a Yau mun tattauna da wadanda abin ya shafa sannan mu ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan yiwuwar samun mafita nan kusa.

Duration:00:14:37

Ask host to enable sharing for playback control

Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro

4/29/2024
Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar. Tafiyar gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare. Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin da taron zai yi wajen magance matsalar yankunan.

Duration:00:13:39

Ask host to enable sharing for playback control

Dalilin Da Fasfo Ya Zama Wajibi Ga Ɗanƙasa Ko Ba Don Tafiya Ba

4/26/2024
Shin ka taba tunanin damammakin da za ka iya rasawa saboda rashin mallakar fasfon dan kasa a Najeriya? Yawancin mutane basu maida hankali wajen mallakar fasfo domin a tunaninsu sai idan kana kokarin ketare kasa ya zama wajibi a gare ka, amma kuma akwai damammaki da za ka iya rasawa saboda rashin mallamar shi. To ku biyo mu cikin Shirin Najeriya a Yau domin jin irin amfanin da mallakar fasfo zai iya muku da kuma damarmakin da za ku iyya rasawa.

Duration:00:13:31

Ask host to enable sharing for playback control

Da Gaske Haƙa Rijiyoyin Burtsatse Na Haifar Da Matsala A Anguwanni?

4/25/2024
Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya. Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?

Duration:00:14:59

Ask host to enable sharing for playback control

Me Ya Sa Ake Ɓoye Wa Mata Wasu Abubuwa Idan Za Su Yi Aure?

4/24/2024
Akwai abubuwan da ya kamata a rika bayyana wa mata idan za su yi aure amma kunya tana hanawa. Wasu sai sun je gidan aure suke tarar da abubuwan da ya kamata ace sun sani daga magabata, amma sai dai su tsinta a wajen kawayensu. Shirin Daga Laraba ya duba dalilan da ya sa ake kin bayyanawa mata wasu mahimman abubuwan da ya kamata su sani idan za su yi aure.

Duration:00:26:46

Ask host to enable sharing for playback control

Yadda Tsananin Zafi Zai Iya Cutar Da Dalibai A Makarantu

4/23/2024
Hukumomi sun bayyana jihohin da za a samu matsanancin zafi a Najeriya. Lamarin ya zo daidai lokacin da makarantu ke komawa hutu, inda ake fargabar yiwuwar yaduwar cututtuka a azuzuwa masu cunkuso. Shin ta wace hanya makarantu za su kauce wa yaduwar cututtuka masu alaka da matsanancin zafi? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani

Duration:00:14:26

Ask host to enable sharing for playback control

Rawar Da NNPP Ke Takawa A Dambarwar Dakatar Da Ganduje

4/22/2024
Dambarwa ta siyasa ci gaba da daukar hankali game da dakatar da shugaban jam’iyar APC na kasa Ana ta takaddama da zargin juna tsakanin jam’iyyun siyasa musamman na Kano da gwamnati mai ci a can. Toh amma wa ke wasa da hankalin wani ko rura wutar rikicin dakatar da Ganduje a jam’iyar APC, Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani a kai.

Duration:00:15:26

Ask host to enable sharing for playback control

Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri Ɗaya

4/19/2024
Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya. Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka? Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.

Duration:00:14:57